• Ministan kudi, Wale Edun ya gabatar da sabon tsarin biyan mafi karancin albashi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Edun ya gabatar da bayanan yadda za a ba ma'aikata albashi da kuma yawan abin zai laƙume da yadda zai shafi kasafin kudi
  • Wannan na zuwa ne bayan kungiyar kwadago ta NLC ta tsunduma yajin aiki domin neman karin mafi karancin albashi a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan kudi a Najeriya, Wale Edun ya gabatar da lissafin mafi karancin albashi ga Shugaba Bola Tinubu.

Wale Edun ya gabatar da lissafin ne a yau Laraba 6 ga watan Yuni bayan ba shi wa'adin awanni 48 da Bola Tinubu ya yi.

Kara karanta wannan

"Karya ne," Gwamnati ta yi magana kan amincewa da biyan albashin akalla N105, 000

Tinubu ya karbi rahoton mafi karancin albashi

Ministan ya gabatar da tsarin albashin ne tare da Ministan kasafi da tsare-tsare, Atiku Abubakar Bagudu, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin takardar da suka mika, sun ba da shawarar biyan N105,000 a matsayin mafi karancin albashi.

A yanzu haka Tinubu yana duba kan bayanan da aka gabatar masa inda ake sa ran zai fitar da sanarwa kan lamarin ba da jimawa ba.

Gwamnatin Tinubu ta yi martani kan jita-jitar

Sai dai kuma Gwamnatin tarayya ta ƙaryata abin da ake ta yadawa kan fitar da yawan kuɗin da aka gabatar.

Gwamnatin ta musanya hakan inda ta bukaci a yi fatali da abin da ake ta yadawa wanda ta tabbatar da cewa bai inganta ba.

Hadimin Shugaba Tinubu kasa a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya tabbatar da haka a shafinsa na X da yammacin yau Alhamis 6 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

Tinubu zai dasa bishiyoyi miliyan 25

A wani Labarin, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatin Najeriya za ta dasa bishiyoyi miliyan 25 daga nan zuwa shekarar 2030.

Wannan na zuwa ne yayin da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka janye yajin aiki a kokarin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi.

Shugaba Tinubu ya kuma ba da tabbacin cewa zai samar da damarmaki ga matasan Najeriya a fannin shuke shuke da ci gaban muhalli.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboNygZRmpKKmmajBonnYmmSmoZuWerOtx6irqGWXlnq1tc2uma5llpaxqnnYmq6apl2gwm6wwGakmpmZoK61rYyzmGarpWK4uK3SmmY%3D